iqna

IQNA

kasar yemen
IQNA - A cikin jawabinsa na mako-mako, jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, yayin da yake sukar matsayar kasashen Larabawa dangane da laifuffukan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi a Gaza, ya dauki matakin "Alkawari na Gaskiya" na Iran a matsayin wani muhimmin abu, kuma wani lamari ne na sauya daidaiton yankin.
Lambar Labari: 3491004    Ranar Watsawa : 2024/04/18

IQNA - Babban kusa a kungiyar Ansarullah ya mayar da martani game da hare-hare da bama-bamai da sojojin kawancen Amurka da Birtaniya suka kai kan garuruwan kasar Yemen.
Lambar Labari: 3490462    Ranar Watsawa : 2024/01/12

San’a (IQNA)  Mohammed Ali al-Houthi mamba a majalisar koli ta siyasa ta kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, ya bayyana amincewa da kudurin da Amurka ta gabatar a kwamitin sulhu kan kasar Yemen dangane da tsaron jiragen ruwa a tekun Bahar Maliya a matsayin wasan siyasa.
Lambar Labari: 3490459    Ranar Watsawa : 2024/01/11

San’a (IQNA) Kungiyar bayar da agaji ta koyar da kur’ani mai tsarki a kasar Yemen ta sanar da kaddamar da taron kasa da kasa na farko na manzon Allah (SAW) na zagayowar ranar wafatin manzon Allah (SAW).
Lambar Labari: 3489870    Ranar Watsawa : 2023/09/24

Riyadh (IQNA) A ranar Alhamis din da ta gabata ne Riyadh ta sanar da cewa ta gayyaci tawagar kungiyar Ansarullah domin kammala tsagaita bude wuta da tattaunawar zaman lafiya.
Lambar Labari: 3489818    Ranar Watsawa : 2023/09/15

Tehran (IQNA) Dalibai miliyan daya da dubu dari biyar ‘yan kasar Yemen maza da mata za su ci gajiyar darussan kur’ani da aka shirya a makarantu da cibiyoyin koyar da kur’ani kusan 9100 na wannan kasa.
Lambar Labari: 3489057    Ranar Watsawa : 2023/04/29

Tehran (IQNA) Majalisar koli ta siyasar kasar Yemen ta fitar da sanarwa a matsayin martani ga cin zarafi da wulakanta kur'ani mai tsarki da ake ci gaba da yi a kasashen Denmark da Sweden, tare da sanya takunkumin hana shigo da kayayyakin da ake samarwa a wadannan kasashe.
Lambar Labari: 3488905    Ranar Watsawa : 2023/04/02

Tehran (IQNA) Mahalarta 4 daga kasashen Afirka daban-daban da ’yan takara biyu daga Indonesia da Yemen ne suka fafata a daren 6 na gasar kur’ani ta kasa da kasa ta Dubai.
Lambar Labari: 3488893    Ranar Watsawa : 2023/03/31

Tehran (IQNA) A cikin wata sanarwa da ofishin siyasa na kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya fitar ya bayyana cewa, sake kulla alaka tsakanin kungiyar Hamas da kasar Siriya ya kara karfafa karfin juriya a yankin.
Lambar Labari: 3488040    Ranar Watsawa : 2022/10/20

Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya ce:
Tehran (IQNA) Yayin da yake ishara da shigar da Amurkawa da Saudiyya suka yi a wannan kasa, jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yaman ya ce: Idan har kawancen 'yan ta'adda ya mamaye sauran yankuna, to za su yi abin da ya fi wannan muni, amma duk da kokarin da suke yi, sun kasa cimma burinsu.
Lambar Labari: 3487885    Ranar Watsawa : 2022/09/20

Tehran (IQNA) Biranen daban-daban na kasar Yemen a yau 8 ga watan Agusta, sun shaida yadda al'ummar wannan kasa suka halarci jerin gwanon Ashura Hosseini tare da nuna goyon baya ga tsayin daka na al'ummar Palastinu.
Lambar Labari: 3487655    Ranar Watsawa : 2022/08/08

Tehran (IQNA) Hukumar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a cikin wani rahoto da ta fitar cewa kimanin ‘yan kasar Yemen miliyan 17 ne ke fama da matsalar karancin abinci, al’amarin da ke kara dagula halin rayuwa a kasar.
Lambar Labari: 3487275    Ranar Watsawa : 2022/05/10

Tehran (IQNA) Ofishin Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Yemen ya ce, ana binciken yiwuwar dakatar da bude wuta a kasar a cikin watan Ramadan.
Lambar Labari: 3487077    Ranar Watsawa : 2022/03/21

Tehran (IQNA) Amurka ta kakaba wasu daga cikin jagororin kungiyar Ansarullah da aka fi sani Alhuthi ta kunkumi.
Lambar Labari: 3486900    Ranar Watsawa : 2022/02/03

Tehran (IQNA) Shugaban tawagar masu shiga tsakani na gwamnatin ceto kasar Yemen ya bayyana cewa: Hadaddiyar Daular Larabawa ba za ta kasance cikin kwanciyar hankali ba, ko da ko ta roki taimako daga Amurka,
Lambar Labari: 3486873    Ranar Watsawa : 2022/01/27

Tehran (IQNA) kungiyar likitocin kasa da kasa ta sanar da cewa, fararen hula akalla 70 ne suka rasa rayukansu a yau a kasar Yemen sakamakon hare-haren da jiragen yakin Saudiyya suka kaddamar a kansu.
Lambar Labari: 3486848    Ranar Watsawa : 2022/01/21

Tehran (IQNA) jiragen yakin gwamnatin kasar Saudiyya sun kaddamar da munanan hare-hare a kan birnin San'a fadar mulkin kasar Yemen a yammacin yau.
Lambar Labari: 3486607    Ranar Watsawa : 2021/11/25

Tehran (IQNA) Abdulmalik Alhuthi shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya bayyana gwagwarmaya domin kare kasa daga makiya a matsayin wajibi na addini.
Lambar Labari: 3486447    Ranar Watsawa : 2021/10/19

Tehran (IQNA) al'ummar kasar Yemen sun fara gudanar da tarukan murnar zagayowar lokacin Maulidin manzon Allah (SAW)
Lambar Labari: 3486415    Ranar Watsawa : 2021/10/12

Tehran (IQNA) an fara aiwatar da wani shiri na koyar da kurame karatun kur'ani mai tsarki a kasar Yemen ta hanyar karatun ishara.
Lambar Labari: 3486251    Ranar Watsawa : 2021/08/29